Home Labaru Wasu Miyagu Na Kokarin Damfarar Nijeriya Biliyoyin Dala – Buhari

Wasu Miyagu Na Kokarin Damfarar Nijeriya Biliyoyin Dala – Buhari

236
0
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shaida wa Majalisar Dinkin Duniya cewa, wasu miyagun kungiyoyin kasa da kasa su na kokarin damfarar Nijeriya biliyoyin kudade na Dala.

Buhari ya bayyana haka ne, yayin da yake gabatar da jawabi a zauren Majalisar, wadda ke gudanar da taron ta karo na 74 a birnin New York na kasar Amurka.

Shugaba Buhari, ya bayyana yarjejeniyar huldar kasuwanci tsakanin kamfanin P&ID na kasar Ireland da gwamnatin Nijeriya a matsayin yunkurin damfarar kasar nan Dala biliyan 9 da miliyan 600.

Idan dai za a iya tunawa, wata kotu Birtaniya ta ba Nijeriya umarnin biyan kamfanin P&ID makudan kudaden, bayan wargajewar yarjejeniyar iskar gas da aka kulla tsakanin bangarorin biyu a shekara ta 2010.