Home Labaru Majalisar Wakilai Ta Tafka Muhawara A Kan Yankunan Da Boko Haram Ta...

Majalisar Wakilai Ta Tafka Muhawara A Kan Yankunan Da Boko Haram Ta Mamaye

183
0
Femi Gbajabiamila, Shugaban Majalisar Wakilai

Majalisar wakilai ta fara yunkurin bude gidauniyar musamman, domin tallafa wa jami’an tsaro ta yadda za su kalubalanci matsalolin tsaro da ke addabar sassa daban-daban na kasar nan.

Kamar yadda Majalisar ta bayyana, abin da aka ware wa hukumomin tsaro a kasafin shekara mai zuwa ya yi kadan a samar da abin da ake bukata a bangaren tsaro.

Matakin dai, ya biyo bayan kudurin da dan majalisa Mohammed Monguno ya gabatar a gaban majalisar, wanda ya sanya wa taken ‘Bukatar Agajin Gaugawa game da yanayin tsaron Nijeriya.’

Dukkan ‘yan majalisar dai sun aminta da wannan kudiri, inda su ka roki gwamnatin tarayya ta kirkiro gidauniyar musamman domin tallafa wa hukumomin tsaro a matsayin kari kan kasafin kasa gaba daya.