Home Labaru Na Bada Cikakken Rahoton Yadda Na Kashe Kudin Majalisar Dattawa – Saraki

Na Bada Cikakken Rahoton Yadda Na Kashe Kudin Majalisar Dattawa – Saraki

240
0
Sanata Bukola Saraki, Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa
Sanata Bukola Saraki, Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa

Tsohon shugaban majalisar dattawa Sanata Bukola Saraki, ya tofa albarkacin bakin sa a kan jita-jitar da ke cewa shi da mataimakin sa Ike Ekwerumadu sun ki bada bayani a kan wasu makudan kudade.

Saraki ya karyata zargin ne ta bakin mai Magana da yawun sa Yusuph Olaniyonu, inda ya ce mai gidan sa ya bada duk bayanan abin da ya faru kafin ya bar ofis.

Olaniyonu, ya ce Saraki ya fitar da bayani a kan duk wasu kudi da aka ware wa ofishin sa domin harkokin gudanarwa, a lokacin da ya ke shugaban majalisa tsakanin watan Yuni na shekara ta 2015 zuwawatan  Mayu na shekara ta 2019.

Yusuph Olaniyonu ya kara da cewa, kafin Bukola Saraki ya bar kujerar majalisa, sai da ya fadi inda duk ya kashe kudaden ofishin sa.

Ya ce an ba Bukola Saraki takardar ajiye aiki mai nuna shaidar cewa, ya bi dokoki da ka’idojin da su ka shafi bada rahoto a kan yadda aka batar da duk wasu kudade a lokacin sa.