Home Labaru Raya Kasa: Gwamna Wike Ya Kalubalanci Gwamnonin Jam’iyyar APC

Raya Kasa: Gwamna Wike Ya Kalubalanci Gwamnonin Jam’iyyar APC

236
0
Nyesom Wike, Gwamnan Jihar Rivers
Nyesom Wike, Gwamnan Jihar Rivers

Gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike, ya kalubalanci gwamnonin jam’iyyar APC su nuna irin ayyukan da su ke yi wa al’ummar su kowa ya gani.

Gwamnan ya bayyana haka ne, yayin da ya ke jawabi a wajen bikin kaddamar da hanyoyi uku da gwamnatin shi ta yi a karkashin jam’iyyar PDP.

Nyesom Wike, ya  ce gwamnonin jam’iyyar PDP ne kadai su ka dage wajen kawo wa jihohin su ayyukan ci-gaba da more rayuwa.

Ya ce Kwanakin baya gwamnan jihar Benue ya gayyace shi domin kaddammar da wasu ayyuka, inda ya je ya kaddamar da akalla tituna guda uku.