Home Labaru Wani Sojan Nijeriya Ya Kashe Kan Sa Da Abokan Aikin Sa Hudu

Wani Sojan Nijeriya Ya Kashe Kan Sa Da Abokan Aikin Sa Hudu

464
0
Buhari Ya Kalubalanci Manyan Hafsoshin Soji Su Kirkiro Sabbin Dabaru
Buhari Ya Kalubalanci Manyan Hafsoshin Soji Su Kirkiro Sabbin Dabaru

Wani sojan Nijeriya da ke aiki da rundunar Lafiya Dole da ke yaki da Boko Haram a yankin arewa maso gabashin Nijeriya, ya kashe abokan aikin sa hudu sannan ya harbe kan sa.

A cikin wata sanarwa da mukaddashin kakakin rundunar sojin Kanar Sagir Musa ya raba wa manema labarai, ta ce sojan wanda ba a bayyana sunan shi ba, ya kuma jikkata wasu abokan aikin shi biyu.

Sanarwar ta kara da cewa, rundunar sojin ta na kokarin tuntubar iyalan sojojin da lamarin ya shafa, sannan ta fara gudanar da bincike domin gano abin da ya haddasa shi.

Sojojin Nijeriya dai su na aiki tukuru wajen yaki da Boko Haram, inda masana harkokin lafiya ke cewa hakan ya na shafar yanayin tunanin su da lafiyar kwakwalwar su.