Home Labaru Takaddama: Dokar Kariya Ta Raba Kawunan ‘Yan Majasalisar Tarayya

Takaddama: Dokar Kariya Ta Raba Kawunan ‘Yan Majasalisar Tarayya

288
0
Takaddama: Dokar Kariya Ta Raba Kawunan ‘Yan Majasalisar Tarayya
Takaddama: Dokar Kariya Ta Raba Kawunan ‘Yan Majasalisar Tarayya

Kudurin dokar da za ta haramta binciken shugabanin Majalisar Dokoki ta Kasa ta raba kawunan ‘yan majalisar, tun kafin a kai ga mika ta ga Kwamitin da zai bude mata fagen saurare a Majalisar Wakilai.

Kudurin, wanda dan majalisa Onorabil Odebunmi Olusegun ya gabatar a zauren Majalisar Wakilai, ya na neman a yi wa sashe na 308 na kundin tsarin mulkin Nijeriya garambawul, domin a ba shugabanin majalisar dokoki na kasa kariya har tsawon zaman su a Majalisar.

Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Wakilai Alhassan Ado Doguwa, ya ce ya na goyon bayan dokar idan har an samu kafa ta.

Dan majalisa Tajuddeen Abbas kuwa cewa ya yi bai ga amfanin kariya ga ‘yan majalisa ba, domin sun je yi wa al’umma aiki ne, don haka y ace ba su bukatar wata kariya.

Manazarci kuma kwararre a kimiyyar siyasa ta kasa da kasa Farfesa Usman Mohammed na Jami’ar Baze da ke Abuja, ya ce kariya ta na sa shugabanni kaucewa, domin gwamnoni da su ka more kariya sun yi amfani da ita ne su ka hau madafun iko demokradiya ta bada damar a hukunta wanda duk aka kama da laifi.