Home Labaru Wani Mahari Ya Kashe Dan Majalisa A Birtaniya

Wani Mahari Ya Kashe Dan Majalisa A Birtaniya

11
0

Wani matashi dauke da wuka, ya hallaka wani dan majalisar Birtaniya dan jam’iyyar Conservative ta Firaminista Boris Johnson, a wani harin da aka kai a gabashin Ingila a yau Juma’a.

Wani matashi dan shekaru 25 ne ya kai hari a kan dan majalisar mai shekaru 69 lokacin da yake ganawa da ‘yan mazabar sa a wata majami’a.

‘Yan sanda sun tabbatar da kama maharin, wanda suka ce shi kadai ne ya aikata wannan danyen aiki.

Dan majalisar wato Sir David Amess mai shekaru 69, dan jam’iyyar Conservative ne ta Firaminista Boris Johnson.

Shaidu sun ce maharin ya daba wa dan majalisar wuka ne a wurare da dama a jikin sa a majami’ar Methodist da ke a gabashin Ingila.

Tun cikin shekarar 1983 ne dai Sir David Amess yake majalisar dokokin na Birtaniya.