Home Labaru Majalisar Dinkin Duniya Ta Ware Ranar 15 Ga Watan Oktoba

Majalisar Dinkin Duniya Ta Ware Ranar 15 Ga Watan Oktoba

10
0

Majalisar Dinkin Duniya ta kebe kowacce ranar 15 ga watan Oktoba, a matsayin ranar matan karkara ta duniya.

An kebe wannan ranar ce domin tunawa da irin gagarumar gudunmawa da mata ke bayarwa  wajen bunƙasa tattalin arziƙin al’ummomi a yankunan karkara.

Tsohon skatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki Moon y ace Karfafawa matan karkara gwiwa na da matukar muhimmanci wajen kawar da yunwa da talauci a tsakanin al’umma.

A shekarar 2012, ne aka kaddamar da wannan rana wadda aka sauyawa suna daga ranar manoma mata ta duniya zuwa ranar matan karkara ta duniya.