Home Labaru Shugaba Buhari Ya Taya Sanata Bashir Garba Lado Murna

Shugaba Buhari Ya Taya Sanata Bashir Garba Lado Murna

43
0

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya taya tsohon Shugaban Hukumar jin dadi da walwalar ‘yan gudun hijira Sanata Basheer Garba Lado murnar cika shekaru 55 a duniya, tare da addu’ar Allah karo masa shekaru masu albarka.


Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a cikin wata takardar sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu ya fitar, kuma aka raba wa manema labarai a nan Abuja.


Shugaban ƙasa ya yi tarayya da sauran ‘ya’yan jam’iyyar APC, da iyalan Sanatan da sauran ‘yan uwa da abokanan arziki, wajen taya zakakurin Sanatan kuma gogaggen ɗan kasuwa wanda ya bada gagarumar gudummawa wajen ciyar da kasa gaba.

Shugaba Buhari ya yi jinjina ta musamman ga tsohon Sanatan kuma tsohon Shugaban hukumar yaki da ayyukan safarrar bil’adama na Najeriya, bisa jajircewar sa wajen samar da ci gaba mai ma’ana a ƙasa.


Shugaban ƙasa ya kuma yi addu’ar kara samun lafiya da kwanciyar hankali ga Sanatan da kuma yi wa iyalan sa addu’a albarka.