Home Labaru Wakilci: Majalisar Dattawa Ta Dawo Ta Kuma Dage Zama Zuwa Ranar Laraba

Wakilci: Majalisar Dattawa Ta Dawo Ta Kuma Dage Zama Zuwa Ranar Laraba

330
0
Wakilci: Majalisar Dattawa Ta Dawo Ta Kuma Dage Zama Zuwa Ranar Laraba
Wakilci: Majalisar Dattawa Ta Dawo Ta Kuma Dage Zama Zuwa Ranar Laraba

Majalisar dattawa ta dawo zama bayan hutun makonni biyar, inda su ka yi ganawar sirri ta tsawon tsawon kimanin sa’a guda, daga bisani sun dage zaman majalisar zuwa ranar Laraba.

Bayan ganawar sirrin, Shugaban majalisar Sanata Ahmad Lawan, ya ce batutuwan da aka tattauna a zaman sun kasance a kan wasu tsare-tsare da ‘yan majalisar za su yi aiki a kai a shekara ta 2020.

Ya ce majalisar dattawa za ta bada muhimmanci sosai a kan magance matsalar tsaro a fadin Nijeriya, kuma za ta yi aiki wajen aiwatar da dokar masana’antun man fetur da gyara dokar zabe.

Sanata Lawan, ya ce majalisar za ta yi hukunci a kan inganta ma’aikatar wutar lantarki, da ci-gaban ma’adinai da kuma habbaka fannin noma a fain Nijeriya.

Hakan dai ya na zuwa ne, yayin da ya yi alkawarin cewa ‘yan majalisar za su yi aiki tare da ma’aikatu, da hukumomi domin tabbatar da aiwatar da cikakken kasafin shekara ta 2020.