Home Labaru Janar Buratai Ya Sake Bude Hanyar Maiduguri Zuwa Damboa

Janar Buratai Ya Sake Bude Hanyar Maiduguri Zuwa Damboa

385
0
Janar Buratai Ya Sake Bude Hanyar Maiduguri Zuwa Damboa
Janar Buratai Ya Sake Bude Hanyar Maiduguri Zuwa Damboa

Shugaban dakarun sojin kasa na Nijeriya Laftanal Janar Tukur Buratai, ya sake bude babbar hanyar Maiduguri zuwa Damboa bayan rundunar soji ta rufe ta saboda rashin tsaro.

Buratai ya bayyana haka ne, a lokacin bikin sake bude hanyar da ay gudana a shingen bincike na Molai, inda ya ce yanzu an bude babbar hanyar ga masu motoci da masu tafiya a kafa da ke zirga-zirga tsakanin Maiduguri zuwa Biu da sauran garuruwa.

Janar Buratai ya ba matafiya da ke bin hanyar tabbacin samun cikakken tsaro, sannan ya umurci dukkan kwamandoji su samar da tsaro ga masu bin hanyar.

Idan dai ba a manta ba, gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Zulum ya yi roko a kan sake bude manyan tituna a lokacin da ya ziyarci ministan tsaro Basir Magashi.