Home Labaru NIS Ta Shawarci Masu Zuba Jari Su Ci Gajiyar Shigowa Nijeriya

NIS Ta Shawarci Masu Zuba Jari Su Ci Gajiyar Shigowa Nijeriya

277
0
NIS Ta Shawarci Masu Zuba Jari Su Ci Gajiyar Shigowa Nijeriya
NIS Ta Shawarci Masu Zuba Jari Su Ci Gajiyar Shigowa Nijeriya

Shugaban hukumar kula da shige da fice na Najeriya, Muhammad Babandede, ya yi kira ga masu zuba jari na gaskiya su ci gajiyar tsarin nan na bayar da biza nan take bayan shigo wa Najeriya.

Babandede, ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa wacce jami’in hulda da jama’a na hukumar, Sunday James, ya fitar a birnin Abuja.

Ya kara da cewa bullo da wannan tsarin zai kuma inganta tabbatar da gaskiya da tsaro a kan ayyukan hukumar ta kula da shige da fice ta Najeriya.

Ya ce Biza tana daya daga cikin abin da kasashe suke amfani da ita domin kula da masu shigowa da kuma magance ayyukan masu fasakwauri.