Home Labaru Ilimi WAEC Ta Riƙe Sakamakon Jarrabawar Ɗalibai 262,803

WAEC Ta Riƙe Sakamakon Jarrabawar Ɗalibai 262,803

177
0

Hukumar shirya jarrabawar kammala karatun sakandare ta
WAEC, ta riƙe sakamakon jarrabawar ɗalibai dubu 262 da
803 da su ka rubuta jarrabawar shekara ta 2023.

Shugaban ofishin hukumar na Legas Patrick Areghan, ya ce an rike sakamakon jarrabawar ne bayan samun dalibai da tafka maguɗi a matakai daban-daban, amma kashi 16 na jimillar ɗaliban da su ka rubuta jarrabawar ne lamarin ya shafa.

Mista Areghan ya kara da cewa, dalilan samun irin wannan matsala a bayyane su ke, domin ɗalibai ba su yi karatu ba su ka dogara da satar amsa yayin jarrabawar.

Ya ce ɗaliban da lamarin ya shafa su na da zaɓin gabatar da kan su domin bincike, da kuma neman damar wanke kan su daga wannan zargi na tafka maguɗin jarabawa kamar yadda aka saba yi a baya.

Leave a Reply