Rahotanni na nuni da cewa, shirin samar da hanyar jirgin kasa
tsakanin Nijeriya da Nijar ya na fuskantar barazana
sakamakon katsewar alaka tsakanin kasashen biyu, biyo bayan
juyin mulkin a ka yi a jamhuriyar Nijar.
Juyin Mulkin dai, sojojin da ke tsaron fadar shugaban kasar Nijar a karkashin jagorancin Janar Abdourahmane Tchiani ne su ka kwace mulki a hannun Muhammed Bazoum.
Fargabar a kan hanyar jirgin kasan dai ta na zuwa ne, ganin yadda manyan motoci sama da dubu 1, wadanda su ka yi dakon kayayyakin da darajar su ta kai sama da naira miliyan 350, wadanda ke kan hanyar shiga Nijeriya da sauran kasashen yammacin Afrika su ka makale a kan iyakokin Nijar.
Idan dai ba a manta ba, tun a shekara ta 2021, gwamnatin Buhari ta bayyana shirin gina layukan jirgin kasa mai nisan kilomita 284 zuwa Nijar daga Nijeriya, wanda a lokacin Nministan sufuri Rotimi Amaechi ya ce za a kashe akalla dala biliyan 2 wajen gina shi.