Home Labaru Majalisa Za Ta Sake Tantance El-Rufa’i Da Sauran Wadanda Ba A Tantance...

Majalisa Za Ta Sake Tantance El-Rufa’i Da Sauran Wadanda Ba A Tantance Ba

94
0

Akwai yiwuwar a sake tantance sunayen Ministoci Uku da
majalisar dattawa ta ki tantancewa da su saboda rahoton tsaro
da aka aike wa majalisar.

Wadanda lamarin ya shafa kuwa sun hada da tsohon gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai, Sanata Abubakar Danladi daga jihar Taraba da tsohuwar shugabar bankin Nexim Stella Okotete.

Kakakin majalisar dattawa Yemi Adaramodu ya bayyana haka, yayin da ya bayyana a wani shirin gidan talabijin na Channels, inda ya ce majalisar za ta sake gayyatar wadanda aka ki amincewa a tantance su idan majalisar ta gamsu da rahoton tsaro da za a aike mata nan gaba.

Ya ce idan hukumar tsaro ba ta gamsu da su ba Majalisa ma ba za ta iya amincewa da su ba, don haka sake gayyatar su ya danganta ne da rahoton hukumar tsaro da kuma ra’ayin shugaban kasa.

Leave a Reply