Home Labaru Wadanda Su Ka Sace Shugaban Makaranta Sun Nemi Fansar Naira Miliyan 20

Wadanda Su Ka Sace Shugaban Makaranta Sun Nemi Fansar Naira Miliyan 20

232
0

‘Yan bindigar da su ka sace Shugaban makarantar sakandaren gwamnati da ke Mararabar Kajuru a cikin karamar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna Mista Francis Maji, sun bukaci a biya kudin fansa naira miliyan 20.

Wata majiya ta bayyana wa manema labarai cewa, masu garkuwar sun tuntubi iyalin sa ta wayar Shugaban makarantar ne su ka gabatar da bukatar su.

Idan ba a manta ba, a tsakar daren ranar Alhamis da ta gabata ne, ‘yan bindigar su ka kai hari makarantar, inda su ka yi garkuwa da Shugaban makarantar kamar yadda rundunar ‘yan sanda ta jihar Kaduna ta tabbatar.

Lamarin dai, ya faru ne mako guda bayan an sace dalibai mata shida, da ma’aikata biyu a kwalejin Engravers College da ke Kakau Daji a karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna.

Wani malamin makarantar da ya nemi a sakaya sunan sa, ya ce ‘yan bindigar da yawan su ya kai sama da 20, sun shiga makarantar ne da misalin karfe 12:00 na dare, sannan su ka fara harbi a sama, daga bisani su ka sace Shugaban makarantar daga gidan sa.