Home Labaru Karin Haske: Kowa Na Iya Zama Dan Shi’a, Amma Ta El-Zakzakky Ba...

Karin Haske: Kowa Na Iya Zama Dan Shi’a, Amma Ta El-Zakzakky Ba – IGP

360
0
Yada Labarai Karya Ne Matsalar ‘Yan Sanda-IG Adamu
Yada Labarai Karya Ne Matsalar ‘Yan Sanda-IG Adamu

Shugaban rundunar ‘yan sandan Nijeriya Mohammed Adamu, ya ce mutane na da ‘yancin kasancewa ‘yan shi’a, amma ba ‘yan haramtaciyyar kungiyar da ke karkashin jagorancin El-Zakzakky ba.

Mohammed Adamu ya bayyana haka ne, yayin wata hira da ya yi da jaridar Daily Trust a Ingila, inda ya kasance daya daga cin  tawagar gwamnatin tarayya da su ka gana da kwararru a fannin doka, tare da ziyartar wasu kafofin yada labaai na kasa da kasa a London, game da kan shari’ar Nijeriya da kamfanin P&ID.

Ya ce tabbas, kungiyar shi’a ta mabiya El-Zakzakky ta ‘yan ta’adda ce, kuma cewa za a yi masu riko na matsayin ‘yan ta’adda. Shugaban ‘yan sandan ya kuma yi Karin haske da cewa, ba dukkan ‘yan Shi’a ake hari ba, kawai wadanda su ka bayyana kan su a matsayin kungiyar mabiya El-Zakzakky ake hari.