Home Labaru El-Rufai Ya Bayyana Kasafin Jihar Kaduna Na Shekara Ta 2020

El-Rufai Ya Bayyana Kasafin Jihar Kaduna Na Shekara Ta 2020

445
0
Nasir El-Rufai, Gwamnan Jihar Kaduna
Nasir El-Rufai, Gwamnan Jihar Kaduna

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai, ya gabatar da Naira biliyan 254 da miliyan 400 a matsayin kasafin kudin jihar Kaduna na shekara ta 2020.

El-Rufa’i, wanda mataimakiyar sa Hadiza Balarabe ta wakilta a wajen wani taron tattaunawa da jama’a game da kasafi shekara ta 2020, ya ce kudin ayyukan da aka soma sun kama Naira biliyan 62 da miliyan 900.

Ya ce, idan aka kaddamar da kasafin, zai bada damar karasa ayyukan da aka soma tare da yin sababbi a mazaunin kashi 72 da kuma 28 cikin 100.

El-Rufai, ya ce Kasafin shekara ta 2020 abu ne da zai ba su damar cimma matsayar ayyuka a gwamnatin su, kuma daga cikin kasafin, an ware naira biliyan 177 da miliyan 29 a matsayin kudin manyan ayyuka.

Akwai kuma naira biliyan 62 da miliyan 900 na ayyukan da aka soma ba a kammala ba. Daga cikin ayyukan da za a yi da kudin kuwa akwai gina sabbin tituna guda 7, da kuma yin kwaskwarima ga wasu guda 14 a birnin Kaduna, baya ga wasu ire-iren su a biranen Kafanchan da Zaria.