Home Labaru Umurnin Gwamnati: ‘Yan Sanda Sun Rufe Wurin Hakar Ma’adanai A Jihar Kano

Umurnin Gwamnati: ‘Yan Sanda Sun Rufe Wurin Hakar Ma’adanai A Jihar Kano

240
0

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano, ta rufe wurin hakar ma’adanai da ke Rimi a cikin karamar hukumar Sumaila domin tabbatar da umarnin da gwamnatin tarayya ta bada.

Gwamnatin tarayya dai ta bada umarnin rufe kowane wurin hakar ma’adanai da ke fadin Nijeriya saboda wasu dalilai na tsaro.

A cikin wata sanarwa da jami’in rundunar DSP Abdullahi Haruna ya fitar, ya ce an tura jami’an tsaro masu yawa zuwa wurin da ake hakar ma’adanan domin bin umarnin da gwamnatin tarayya ta bada.

DSP Haruna, ya ce hukumar ‘yan sanda ta jihar Kano ta tura jami’an ta su ziyarci wurin hakar ma’adanan domin tabbatar da cewa mutanen yankin sun bi doka.

Haka kuma, DSP Haruna ya bukaci al’umma su yi hakuri su bi doka har zuwa lokacin da gwamnati za ta bude wurin.