Home Labaru Matakan Tsaro: Buhari Ya Umurci Shugabannin Tsaro Su Yi Aikin Ba Sani...

Matakan Tsaro: Buhari Ya Umurci Shugabannin Tsaro Su Yi Aikin Ba Sani Ba Sabo

343
0

Rahotanni na cewa, Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya umarci hukumomin tsaro cewa kada su rangwanta wa duk masu haifar da ta’addanci a jihar Zamfara da kewayen ta da ma sauran sassan Nijeriya.

Shugaban ma’aikatan tsaro na kasa Janar Gabriel Olanisakin ya bayyana wa manema labarai haka a fadar shugaban kasa da ke Abuja, jim kadan bayan ganawar su da ta tsawon sa’o’i biyu da shugaba Buhari.

Da yak e bada rahoton matakan tsaron da hukumar ‘yan sanda ta dauka, mukaddashin shugaban rundunar ‘yan sandan Nijeriya Muhammadu Adamu, ya ce a halin yanzu hanyar Abuja zuwa Kaduna ta tsarkaka daga ta’addancin masu garkuwa da mutane.

Leave a Reply