Home Labaru Zargin Cuwa-Cuwa: An Kori ‘Jami’an Yan Sanda 9, An Rage Ma 6...

Zargin Cuwa-Cuwa: An Kori ‘Jami’an Yan Sanda 9, An Rage Ma 6 Girman Mukami

261
0

Hukumar Kula Da Ladabtar Da jami’an ‘Yan Sanda Ta Kasa ta kori wasu manyan jami’an ta guda 9, tare da rage ma wasu manyan jami’ai shida mukamai.

Hakan dai, ya biyo bayan samun su da laifin tabka harkalla da cuwa-cuwa wajen daukar kananan sabbin jami’an ‘yan sanda tun cikin shekara 2011.

Kakakin hukumar Ikechukwu Ani ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Abuja.

Ani ya ce, wadanda korar ta shafa sun hada da wani Abdul Yahaya Ahmed da Adamu Damji Abare da Osondu Christian, da Pious Timiala, da Agatha Usman da kuma Hassan Dass.

Wadanda aka rage ma girman mukami kuma sun hada da Oluwatoyin Adesupe da Mansir Bako da Gbenle Mathew da Tijjani Saifullah da Sadiq Idris da kuma Alice Abbah.

An dai yanke masu hukuncin ne a wajen taron da Hukumar ta gudanar karo na biyar a Abuja.