Home Labaru Umurni: A Fara Laluben Watan Sha’aban A Ranar Juma’a – Sultan

Umurni: A Fara Laluben Watan Sha’aban A Ranar Juma’a – Sultan

854
0
Sarkin Musulmi Abubakar Sa’ad II
Sarkin Musulmi, Abubakar Sa’ad II

Mai alfarma Sarkin Musulmi Abubakar Sa’ad III, ya bukaci a fara duban watan Sha’aban a ranar Juma’ar nan.

Sarkin Musulmi ya yi kiran ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban kwamitin fadar sa a kan harkokin da su ka shafi addini Farfesa Sambo Junaidu.

Farfesa Junaidu ya yi shelar fara duba jaririn watan a ranar Juma’ar nan, wadda ta yi daidai da ranar 29 ga watan Rajab na Kalandar Musulunci a shekara ta 1440.

A cewar sa, ana neman Musulmin Nijeriya su sa ido wajen duban sabon watan, tare da gaggauta shigar da rahoton ganin sa zuwa ga Dagaci ko kuma Mai Unguwa na kusa da su.

Yayin da watan Azumin Ramalana ke biyo bayan watan Sha’aban, Sultan ya roki Allah ya shige wa dukkan Musulmi gaba wajen sauke nauyin Bautar da rataya a wuyan su a matsayin bayin sa.

Leave a Reply