Home Labaru Kiwon Lafiya Kiwon Lafiya: Nijeria Na Rasa Naira Biliyan 400 A Kan Neman Magani...

Kiwon Lafiya: Nijeria Na Rasa Naira Biliyan 400 A Kan Neman Magani A Kasashen Waje – Buhari

375
0
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari

Shugaban kasa Muhamadu Buhari, ya koka da yadda ‘yan Nijeriya ke kashe makudan kudade a kowacce shekara wajen neman magani a kasashen ketare.

Buhari ya bayyana damuwar sa ne, yayin kaddamar da taron kara wa juna sani na manyan shuwagabannin cibiyar nazarin tsare-tsare ta kasa.

Shugaba Buhari, wanda ya samu wakilcin gwamnan jihar Filato Simon Lalong, ya yi kira ga mahalarta taron su gano hanyoyin magance gibi da matsalolin da ake samu a cibiya, domin bunkasa sa hannun jari a ilimin kasa.

Ya karfafa gwiwar su a kan ci-gaba da bincike da neman karin ilimi a kan yadda kasashen Afrika da Asia da Tarayyar Turai da Amurka ke daukar nauyin bunkasa fannin lafiyar su, da kuma yadda binciken su zai amfani Nijeriya.

Shugaba Buhari, ya ce gwamnatin sa ta dukufa wajen ganin ta bunkasa fannin lafiya da rage yawan kudaden da ake kashewa a kan neman lafiya a wasu kasashe, ya na mai cewa gwamnatin sa ta samar da Naira biliyan 55 a shekara ta 2018, domin zuba jari a asibitocin Nijeriya kamar yadda ya ke a dokar lafiya ta kasa da aka sa wa hannu a shekara ta 2014.

Leave a Reply