Gwamnatin tarayya, ta batar da kimanin Naira biliyan 300 wajen shirye-shiryen tallafin inganta jin dadin rayuwar al’umma musamman Matasa da Mata.
Babbar mai ba shugaban kasa shawara a kan harkokin shirin tallafin inganta jin dadin rayuwa Maryam Uwais ta bayyana haka a Abuja, yayin da ta karbi bakuncin kwamitin yaki da talauci na Majalisar dattawa.
Sanata Lawal Gumau da kuma dan majalisar wakilai Muhammad Wudil ne su ka jagoranci tawagar kamar yadda rahotanni su ka bayyana.
Maryam Uwais, ta ce shirin tallafin inganta jin dadin rayuwar Matasa da Mata da gwamnatin shugaba Buhari ta assassa tun a shekara ta 2016 ya taimaka kwarai, yayin da kimanin mutane miliyan 20 na al’ummar Nijeriya ke cin moriyar shirin. Ta ce gwamnatin shugaba Buhari ta na ciyar da kimanin daliban Makarantun Firamare da Sakandare miliyan 9 da rabi, musamman a wasu yankunan Arewa da ke fuskantar kuncin rayuwa.