Home Labaru Umarnin Kotu: INEC Ta Ce Zata Kalubalanci Ba Okorocha Shaidar Lashe Zabe

Umarnin Kotu: INEC Ta Ce Zata Kalubalanci Ba Okorocha Shaidar Lashe Zabe

237
0
Hukumar Zabe Mai Zaman Kan Ta kasa, INEC
Hukumar Zabe Mai Zaman Kan Ta kasa, INEC

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta ce za ta daukaka kara kan hukuncin da kotu ta bada na tilasta mata ba tsohon gwamnan Jihar Imo Rochas Okorocha takardan shaidar cin zabe.

Okorocha ya karbi takardar shaidan lashe zabe a matsayin wanda ya yi nasara a zaben sanata mai wakiltan Imo ta Yamma a zaben da aka gudanar a ranar 23 ga watan Fabrairu.

INEC ta bayyana hakan ne cikin a cikin wata sanarwa da Kwamishinan yada labaran ta na kasa Festus Okoye ya fitar a Abuja.

Okoye ya ce hukumar INEC ta ba Okorocha takardar shaidan cin zabe ne domin yin biyaya ga umurnin babbar kotu da ke Abuja.

Ya ce INEC ta cimma matsayar ba Okorocha shaidan lashe zaben ne a ranar Talatar da ta gabata bayan sun yi taron tattaunawa a kan wasu dalilai 14 da suka shafi batutuwan zaben.