Home Labaru Ta’addanci: Mayakan Boko Haram Sun Kashe Mutane 26 A Kamaru

Ta’addanci: Mayakan Boko Haram Sun Kashe Mutane 26 A Kamaru

689
0

Mayakan kungiyar Boko Haram da ke kai hare-hare a Najeriya sun kashe a kalla mutane 26 a wani mummunan hari da suka kai a kasar Kamaru a cewar wata majiya daga hukumomin tsaro.
“An kashe sojoji 17 da farar hula 9” cikin wani hari da aka kai a safiyar ranar Litinin a wani tsibiri da ke kasar Kamaru kusa da Tafkin Chadi, kamar yadda jami’in tsaro ya shaidawa AFP.
Da farko, a ranar Litinin an ruwaito cewa sojojin Kamaru uku ne aka kashe a harin tare da farar hula da ba a tabbatar da adadin su ba a wata harin da aka kai a sansanin sojoji.
Jami’in tsaron ya shaidawa AFP a ranar Talata cewa harin na Boko Haram ya yi janyo bata kashi tsakanin sojin Kamaru da ‘yan ta’addan.
Ya ce an kama ‘yan ta’addan 40 kuma an nemi sojoji bakwai an rasa. Majiyar ya ce ‘yan ta’addan sun kafa tutarsu a Darak kafin daga bisani sojoji suka fattake su.
Kungiyar ta Boko Haram ta dade tana yunkurin kafa daular musulunci a Arewa maso Yammacin Najeriya kuma daga bisani sun fara yaduwa zuwa kasashen da ke makwabtaka da Najeriya kamar Chadi da Kamaru.
‘Yan ta’addan sun kashe a kalla mutane 27,000 tare da raba mutane miliyan 1.8 da muhallinsu. An kafa sojojin hadin gwiwa tsakanin kasahen Chadi, Kamaru, Jamhuriyar Nijar da Najeriya

Leave a Reply