Home Labaru Samar Da Tsaro: Sojoji Sun Gano Shirin Kungiyar ISWAP Na Daukar...

Samar Da Tsaro: Sojoji Sun Gano Shirin Kungiyar ISWAP Na Daukar Sabbin Mayaka

711
0

Dakarun rundunar tsaro ra hadin gwiwa ta kasa da kasa sun gano wani shiri da kungiyar ‘yan ta’adda ta ISWAP ke kokarin yi na fara daukar sabbin mayaka cikin watanni masu zuwa ta hanyar yada da’awar karya da juya tunanin matasa.

Kakakin rundunar kanal Timothy Antigha ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya bukaci sarakunan gargajiya da shugabanin addinai da iyaye su sa ido a kan ‘ya ‘yan su domin kare su daga sharrin ‘yan ta’addan.

Ya ce kungiyar ta’addancin ISWAP na shirin fara yada labaran karya da farfaganda domin kada su rasa mayaka, saboda yadda dakarun sojojin suka hallaka mutanan su da dama a wasu makonnin da suka gabata.

Kanal Antigha ya kuma karya ta ikirarin da ‘yan ta’addan su ka yin a cewa sun kai hari a sansanin sojoji da ke Nijeriya da Jamhuriyar Nijar cikin mujallar NABA a ranar 7 ga watan Yuni.

Leave a Reply