Home Labaru Gidan Kaso: Gwamna Ortom Ya Yi Wa Fursunoni 500 Afuwa A Jihar...

Gidan Kaso: Gwamna Ortom Ya Yi Wa Fursunoni 500 Afuwa A Jihar Benue

296
0

Gwamna Samuel Ortom na Jihar Benue, ya yi wa fursunoni sama da 500 afuwa a cikin shekaru hudu kamar yadda Kwamishinan Shari’a na jihar Micheal Gusa ya tabbatar.

Gusa ya shaida wa manema labarai cewa, dukkan wadanda aka yi wa afuwar ‘yan asalin jihar Benue ne.

Ya ce daga cikin wadanda aka yi wa afuwar akwai fursunoni 250 da aka tsare tare da ba su zabin biyan tara maimakon daurin da aka yi masu, amma su ka kasa biya ballantana a sake su.

Sannan akwai wasu da aka yi wa daurin rai-da-rai da kuma wadanda aka yanke wa hukuncin kisa.

Gwamna Ortom ya kuma ja kunnen matasa su daina shiga harkokin aikata miyagun laifuffuka da nufin neman abinci.