Home Labaru Tuhuma: Zakzaky Da Dasuki Sun Fi Son Ci-Gaba Da Zama Hannun Mu...

Tuhuma: Zakzaky Da Dasuki Sun Fi Son Ci-Gaba Da Zama Hannun Mu A Kan Kurkuku – DSS

315
0
Hukumar Tsaro Ta Farin Kaya, DSS
Hukumar Tsaro Ta Farin Kaya, DSS

Hukumar tsaro ta farin kaya DSS, ta bayyana dalilin da ya sa ta ke ci-gaba da rike Kanar Sambo Dasuki, da Sheikh Ibrahim Zakzaky da jagoran gangamin juyin-juya-hali Omoyele Sowore.

Idan dai ba a manta ba, DSS ta ki sakin mutanen uku, duk kuwa da cewa su na fuskantar shari’u a kotuna daban-daban, sai dai ta ce mutanen sun gwammace ci-gaba da zama a hannun ta fiye da zaman gidan yari.

Kakakin hukumar Peter Afunanya ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce Zakzaky da Dasuki da Sowore ne su ka roki kotu ta taimaka su cigaba da zama a hannun DSS maimakon a kai su Kurkuku.

Ya ce a wajen su, su na samun damar ganawa da mutanen su, kuma su na amfani da wayoyin salula, su na kallon talabijin, su na karatun jaridu, su na da damar shiga dakin motsa jiki, su na samun kulawa a asibitin su, sannan iyalan su na kai musu abinci.

A ya ce hukumar ta ce za ta cigaba da aiki hannu da hannu da kafafen yada labarai da yan jarida wajen ilimantar da jama’a game da ayyukan ta.