Home Labaru Raddi: Omokri Ya Caccaki A’isha Buhari Game Da Nema Wa Gwamnan Kogi...

Raddi: Omokri Ya Caccaki A’isha Buhari Game Da Nema Wa Gwamnan Kogi Gafara

269
0
Reno Omokri, Tsohon Hadimin Shugaban Kasa Goodluck Jonathan
Reno Omokri, Tsohon Hadimin Shugaban Kasa Goodluck Jonathan

Tsohon hadimin shugaban kasa Goodluck Jonathan, Reno Omokri, ya kalubalanci uwargidar shugaban kasa A’isha Buhari game da magiyar da ta yi wa jama’an jihar Kogi cewa su gafarta wa Yahaya Bello.

Omokri ya bayyana haka ne a shafin sa na Twitter, inda ya ce idan har A’isha na son jama’ar Kogi su gafarta wa Yahaya Bello to ta fara yafe wa Mamman Daura da iyalan sa.

A’isha Buhari dai ta nemi jama’ar jihar Kogi su gafarta wa Yahaya Bello ne, biyo bayan rashin biyan albashin ma’aikata da gwamnatin sa ta yi tsawon shekara da shekaru, yayin da ya ke neman zarcewa a kan kujerar mulki karo na biyu.

Uwargidan shugaban kasa, ta tabbatar wa al’ummar Kogi cewa Yahaya Bello zai biya bashin albashin ma’aikatan saboda shugaba Muhammadu Buhari ya shiga cikin maganar, tare da ba su tabbacin cewa ba zai sake ba su kunya ba.

Sai dai Reno Omokri ya yi bara’a da ra’ayin ta, inda ya ce idan har ta na son mutanen Kogi su yafe wa Yahaya Bello, mutumin da ya kwashe shekaru ba tare da biyan albashi ba to ta fara gafarta wa Mamman Daura da iyalan sa, ta kuma dawo da su cikin fadar shugaban kasa.