Fitaccen mai rajin kare hakkin bil-Adama, Femi Falana, ya ce yadda gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ke kuntata wa ‘yan jarida manuniya ce ta shirin neman zarcewa a kan mulki karo na uku.
Falana ya bayyana haka ne, yayin da ya ke gabatar da kasida a wajen taron kaddamar da wani littafi mai taken ‘Testimony to courage’ a Turance, wanda aka wallafa a kan shugaban kamfanin jaridar Premium Times Dapo Olorunyomi, a jihar Legas.
Ya ce Nijeriya na cikin mawuyacin hali, don haka bai kamata kafafen yada labarai su yi shiru ba, kuma nan ba da jimawa ba watakila a fara jin an fara kokarin neman tazarce karo na uku.
Lauyan ya kara da cewa, ba za su bari a lalata kafafen yada labarai ba, kuma babu wani mai mulkin kama karya da ya isa ya danne ‘yan Najeriya.
A
karshe ya bayyana damuwar sa da yadda Alkalin babbar kotun tarayya da ke a
Legas mai shari Ijeoma Ojukwu ke gudanar da shari’ar Omoyele Sowore, inda ya ce
bai taba ganin irin sharuddan belin da ta gindaya ma shi ba.