A cikin watan Oktoba ne, Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar da kudirin dokar kasafin shekara ta 2020 a gaban majalisun dokoki na tarayya, wanda kunshi naira tiriliyan 10 da biliyan 300.
Sai dai bayan nazarin majalisar dokokin ta kasa, Buhari ya sanya hannu ne a kan kudirin da ya kunshi naira tiriliyan 10 da biliyan 600, inda aka samu karin da ya kai naira biliyan 264.
Shugaban kwamitin kasafi na majalisar dattawa Ibrahim Barau, ya ce anyi cushe a kasafin ne domin toshe gibin da aka samu wajen samar da ayyuka Nijeriya.
Kamar yadda ya ke kunshe a cikin kasafin, birnin tarayya Abuja ya fi samun kaso mai tsoka daga cikin hukumomi da ma’aikatun gwamnatin tarayya.
Tun farko shugaba Buhari ya kasafta wa birnin Abuja naira biliyan 28 da miliyan 400, amma da kudirin kasafin ya zama doka, sai yawan kudaden ya karu zuwa naira biliyan 62 da miliyan 41.
A cikin kasafin dai, kusan duk ma’aikatun Nijeriya sun samu kari daga majalisar dokokin, abin da masharhanta ke kira cushe.