Home Labaru Hakimin Birnin Gwari Ya Kubuta Daga Masu Garkuwa Da Mutane

Hakimin Birnin Gwari Ya Kubuta Daga Masu Garkuwa Da Mutane

422
0

Hakimin Birnin Gwari Alhaji Yusuf Yahaya da aka yi garkuwa da shi ta hanyar ranar 18 ga watan Disamba ya kubuta da safiyar Juma’ar nan.

An dai yi garkuwa da Hakimin ne a kan hanyar sa ta zuwa wani wuri da aka kebe domin yin sulhu tsakanin al’ummar Birnin Gwari da masu sata da kisan jama’a a yankin.

A cikin wata sanarwa da matasan yankin Birnin gwari su ka fitar, ta ce Hakimin ya tsira ne daga hannun masu garkuwar a kauyen Sabon Birni da ke bayan filin jirgin sama na jihar Kaduna.

Basaraken ,ya kuma aike wa wani makusancin sa sakon wayar hannu da misalin karfe 5:30 na asuba da ya je ya dauke shi.

Sanarwar ta kara da cewa, hakimin ya tsere ne daga inda ya ke tsare, a lokacin da masu garkuwa da shi ke sharar barci.