Home Labaru Matukan Adaidaita Sahu Sun Tafka Asarar N300M Bayan Shiga Yajin Aiki

Matukan Adaidaita Sahu Sun Tafka Asarar N300M Bayan Shiga Yajin Aiki

58
0

Kiyasi na nuni da cewa, yajin aikin da matuka Keke NAPEP su ka shiga a jihar Kano, ya janyo asarar a kalla harajin naira miliyan 6 da jihar ke samu a kowace rana na naira 100 ga kowane mutukin adaidaita Sahu a jihar.

 A bangaren matukan adaidaita sahun kuwa, kiyasi ya nuna sun tafka asarar akalla Naira miliyan 300 kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Matuka Keke NAPEP dai sun yi zanga-zanga ne akan karin kudin rijista da hukamar kula da tituna wato KAROTA ta yi, inda ta koma karbar Naira dubu 18 da ga sabbin masu rijista, yayin da ta koma karbar Naira dubu 8 ga masu sabunta rijista duk shekara.

 Shugaban kungiyar matuka A Daidaita Sahu na jihar Kano Sani Sa’idu Dankoli, ya ce asalin matsalar da ta sa su cikin wannan yanayin shi ne yadda gwamnatin tun farko ta sa Naira dubu 20 a kan kowane matukin Keke NAPEP duk shekara.

Ya ce har yanzu su na magana da ‘yan kungiyar domin janye yajin aikin, domin da yawan su ba su da abin da za su ci da iyalan su in dai ba su fita sun nema a kullum ba.