Home Labaru Tsohon Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari Ya Koma Mahaifar Sa, Daura

Tsohon Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari Ya Koma Mahaifar Sa, Daura

31
0

Bayan mika mulki ga Bola Ahmed Tinubu a matsayin wanda
zai gaje shi, tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya
sauka a mahaifar sa garin Daura da ke jihar Katsina.

Shugaba Buhari dai ya tashi a jirgin sama tare da mai dakin sa A’isha Buhari da wasu daga cikin ‘ya’ya da dangi da kuma ministan sufurin jiragen sama mai barin-gado Hadi Sirika, daga filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja bayan sun bar dandalin Eagle Square ne.

Sabon gwamnan jihar Katsina Dakta Dikko Radda ne ya tarbi tsohon shugaban kasar da tawagar sa a babban filin jirgin sama na Ummaru Musa Yar’adua da ke Katsina.

Jirgin ya sauka a Katsina ne da misalin karfe1:10 na rana, bayan hutun wasu mintina Buhari da matar sa da dan sa Yusuf da wasu shugabannin hukumomin tsaro su ka hau wani jirgi mai saukar ungulu zuwa garin Daura.

Leave a Reply