Home Labaru Dandamalin Rantsar Da Abba Gida-Gida Ya Rufta

Dandamalin Rantsar Da Abba Gida-Gida Ya Rufta

514
0

Dandamalin da aka rantsar da sabon gwamnan jihar Kano
Injiniya Abba kabir Yusuf, ya rufta a daidai lokacin da ake
gudanar da bikin karbar rantsiwar.

Lamarin dai ya faru ne a lokacin da sabon gwamnan ya ke a kan dandamalin tare da matimakin sa da mukaddashin babban mai shari’a na jihar, wanda ya jagoranci rantsar da sabon gwamnan da mataimakin sa, sai dai babu wanda ya ji rauni a cikin su.

Abba Gida-gida dai ya na shirin barin dandamalin ne bayan an rantsar da shi nan take ya rufta, inda jami’an tsaro su ka kakkare shi ciki har da kwamishinan ‘yan sanda na jihar Ahmad Gumel.

An dai katse bikin ta yadda sabon gwamnan bai iya duba faretin masu kayan sarki ba, saboda cincirundon magoya baya da su ka yi wa filin wasa na Sani Abacha cikar-kwari ciki da waje.

Leave a Reply