An fara samun dogayen layuka a gidajen man fetur da ke birnin Lagos, jim kadan bayan sanarwar da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi ta janye tallafin man fetur.
Rahotanni sun ce, direbobin motoci sun yi cincirindo a gidajen mai na NNPC da ke Ikeja inda su ke rige-rigen sayen man.
Wata majiya ta ce, da dama daga cikin gidajen man fetur masu zaman kan su ba su saida man ya zuwa lokacin da rahoton ya bayyana.
A jawabin sa na karbar rantsuwar kama aiki dai, shugaba Tinubu ya ce mawadata ne kadai ke amfana da kudin tallafin man fetur maimakon talakawa.
Ya ce gwamnatin shi za ta karkatar da kudin tallafin zuwa ga bangarorin ilimi da lafiya da samar da ayyuka da gina kayayyakin more rayuwa da za su amfani miliyoyin al’umma. Kuma, shugaba Tinubu ya ce zai nazarci korafe-korafe game da dimbin kudaden haraji, domin ganin an habbaka tattalin arzikin Nijeriya tare da janyo masu zuba jari














































