Home Labaru Tsohon Gwamna Ya Sauya-Sheka Tare Da Magoya Bayan Sa

Tsohon Gwamna Ya Sauya-Sheka Tare Da Magoya Bayan Sa

15
0

Tsohon gwamnan jihar Ondo Olusegun Mimiko ya koma jam’iyyar PDP, bayan wani zama da ya yi da gwamnonin jam’iyyar a karkashin jagorancin Aminu Waziri Tambuwal.

Dr. Olusegun Mimiko dai ya fice daga jam’iyyar Zenith Labour Party, wadda ya kafa bayan ya sauya-sheka gabanin zaben shekara ta 2019.

Shugaban jam’iyyar ZLP na rjihar Ondo Joseph Akinlaja ya tabbatar da sauyin shekar, inda ya masu ruwa da tsaki a jam’iyyar daga kananan hukumomi 18 da ke jihar Ondo sun amince su shiga jam’iyyar PDP.

Wadanda su ka halarci taron sauya shekar kuwa sun hada da tsohon gwamna Mimiko, da Agboola Ajayi da Gboye Adegbenro da tsohon shugaban majalisar dokoki na jihar Ondo Jumoke Akindele.

Akinlaja, ya ce da shi da sauran jiga-jigan jam’iyyar ZLP sun amince su sauya-sheka zuwa jam’iyyar PDP, domin su ceto Nijeriya daga mulkin gwamnatin jam’iyyar APC.