Home Labaru Sojoji Sun Sami Nasarar Halaka ‘Yan Ta’adda Sama Da 30 A Jihar...

Sojoji Sun Sami Nasarar Halaka ‘Yan Ta’adda Sama Da 30 A Jihar Borno

18
0
Soldiers and policemen walk past burnt house on February 4, 2016 during a visit to the village of Dalori village, some 12 kilometres from Borno state capital Maiduguri, northeastern Nigeria, after an attack by Boko Haram insurgents on the village left at least 85 people dead on January 30, 2016. At least 85 people died when Boko Haram insurgents stormed and torched a village on January 30 near the restive northeast Nigerian city of Maiduguri, a state commissioner said on February 1, 2016. Boko Haram, which seeks a hardline Islamic state in northern Nigeria, has killed some 17,000 people and forced more than 2.6 million others to flee their homes since 2009. / AFP / STRINGER (Photo credit should read STRINGER/AFP/Getty Images)

Rundunar sojin Nijeriya, ta samu nasarar hallaka sama da ‘yan ta’adda 30, bayan wani samame da dakarun hadin gwiwa su ka kai wata maboyar su a jihar Borno.

Kakakin rundunar sojin Birgediya Janar Onyema Nwachukwu, ya ce farmakin wani bangare ne na kara kaimin da sojoji ke yi, domin kawo karshen matsalolin tsaro a yankin Arewa maso gabas da sauran sassan Nijeriya.

Janar Nwachukwu, ya ce a ranar Asabar da ta gabata ne, ‘yan kungiyar sa-kai su ka lura da zirga-zirgar wasu manyan motocin yaki masu bindigogi guda shida a cikin dajin Sambisa, wadanda daga bisani su ka kasance a wani kauye kusa da garin Yuwe.

Ya ce bayan haka ne manyan motocin masu dauke da bindigogin su ka koma wani wuri mai nisa, inda wasu ‘yan ta’adda su ka hadu da sauran wadanda su ka tuko motocin a wani abu mai kama da taron mayaka.

Rahotanni sun yi nuni da cewa, sama da mayakan Boko Haram da na ISWAP 50 ne aka hangi sun taru a wajen taron, kuma bayan gano maboyar su nan take sashen mayakan sama ya tura jiragen sama guda biyu domin gudanar da bincike a kan wurin, sannan aka dauki matakan da su ka dace.