Home Labaru Tsirarun Mutane Daga Jihohi 5 Ne Su Ka Tattara Arzikin Nijeriya –...

Tsirarun Mutane Daga Jihohi 5 Ne Su Ka Tattara Arzikin Nijeriya – Buhari

642
0
Shugaban kasa Muhammadu Buhari
Shugaban kasa Muhammadu Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce mafi yawan arzikin Nijeriya ya na tattare ne a hannun wasu ‘yan tsirarun mutane, wadanda su na zaune ne a jihohi hudu zuwa biyar idan aka hada da birnin tarayya Abuja.

Buhari ya bayyana haka ne, yayin da ya ke gabatar da jawabi a wajen biki bude wani taron tattalin arzikin kasa da ake yi a Abuja.

Ya ce yayin da masu arzikin ke zaune a jihohin Nijeriya biyar, akwai ragowar ‘yan Nijeriya kusan miliyan 150 da ke zaman jiran samun ingantacciyar rayuwa a sauran jihohi.

Shugaba Buhari ya kara da cewa, kafin jama’ar wata al’umma su zama masu rufin asiri, sai ya kasance mafi yawan jama’a su na rayuwa cikin sukuni. Ya ce gwamnatin sa ta fahimci cewa, akwai bukatar ‘yan Nijeriya su zama masu rufin asiri, kuma hakan ne ya sa gwamnatin sa ta dauki matakan rage rashin aiki da radadin talauci.