Home Labaru Kotu Ta Fara Sauraren Karar Da Aka Shigar Da Buhari A Kan...

Kotu Ta Fara Sauraren Karar Da Aka Shigar Da Buhari A Kan Osinbajo

251
0

Wata kotun tarayya da ke zama a Legas, ta fara zaman sauraren karar da wani lauya mazaunin jihar Legas Inihebe Effiong ya shigar a kan shugaba Buhari, sakamakon kin mika mulki ga mataimakin sa Farfesa Yemi Osinbajo yayin da ya yi bulaguro zuwa kasar Ingila daga ranar 25 ga watan Afrilu zuwa 5 ga watan Mayu na shekara ta 2019.

An dai sanya sunan ministan shari’a kuma babban lauyan gwamnatin tarayya Abubakar Malami daga cikin wadanda ake kara.

Lauya Effiong ya nemi kotun ta yi duban tsanaki bisa dogaro da sashe na 145 (1) na kundin tsarin mulkin Nijeriya, wajen zartar da hukunci a kan lamarin.

Sai dai shugaba Buhari da Abubakar Malami sun bayyana cewa, doka ta ba shugaban kasa wa’adin kwanaki 21 ya rubuta irin wasikar da lauyan ya ambata ga shugabannin majalisun dokoki na tarayya. Lauyoyin shugaba Buhari sun musanta, tare da kalubalantar lauya Effiong cewa shugaba Buhari ya ziyarci kasar Ingila ne domin hutawa, tare da rokon kotun ta yi watsi da karar da lauyan ya shigar.