Home Labaru Kiwon Lafiya Cutar Shawara: EU Ta Ba Jihohin Katsina Da Bauchi Tallafin Miliyoyin Naira

Cutar Shawara: EU Ta Ba Jihohin Katsina Da Bauchi Tallafin Miliyoyin Naira

378
0

Tarayyar kasashen Turai EU, ta agaza wa jihohin Katsina da Bauchi da tallafin Naira miliyan 31 domin dakile yaduwar zazzabin shawara a jihohin.

Idan dai ba a manta ba, a watan Satumba ne aka sanar da bullar cutar a wadannan jihohi biyu, inda a kalla mutane 27 su ka kamu da cutar yayin da wasu ma sun rasu.

Bincike ya nuna cewa, mutane sun kamu da cutar ne bayan sun dawo daga ziyara a dajin Yankari da ke jihar Bauchi.

Duk da tarin magungunan allurar riga-kafin cutar da Nijeriya ke samu, binciken ya nuna cewa jihohin kasar nan da birnin tarayya Abuja sun yi fama da cutar a shekara ta 2019. Tarayyar kasashen Turai ta bayyana cewa, ta bada kudaden ga kungiyar bada agaji ta ‘Red Cross International’, domin ganin an kashe su ta hanyoyin da ya kamata a wadannan jihohi.