An sako ƙarin ɗalibai goma na makarantar sakandire ta Bethel Baptist dake Kaduna daga hannun ƴan bindiga.
Mataimakin Shugaban Ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN), Joseph Hayab ya tabbatar wa BBC cewa an sako ɗaliban ne ranar Lahadi kuma kawo yanzu akwai sauran ɗalibai 11 a hannun ƴan bindigar.
Mista Hayab ya ce tuni aka miƙa ɗaliban ga iyayen su.
A makon da ya gabata ne ran 18 ga watan Satumba ƴan bindigar suka sako wasu ɗaliban 10 bayan sun kwashe sama da kwanaki 70 a hannun su.
You must log in to post a comment.