Home Labaru Kare Kai: Basarake A Sakwkwato Ya Rantse Da Alkur’Ani Ba Ya Taimaka...

Kare Kai: Basarake A Sakwkwato Ya Rantse Da Alkur’Ani Ba Ya Taimaka Wa ’Yan Bindiga

14
0

Wani basarake a jihar Sakwkwato ya mike a masallacin Juma’a sannan ya rantse da Alkur’ani mai girma cewa ba ya taimaka wa ayyukan ’yan bindiga ta kowacce fuska a masarautar sa.

Basaraken, wanda shi ne Hakimin Isa, kuma Sarkin Gobir din Isa, Alhaji Nasir Ahmad ya rantse da Alkur’anin ne a masallaci biyo bayan zargin da wasu mazauna yankin ke yi masa na alaka da ’yan ta’adda.

Rahotnanni sun ce Hakimin ya mike a Masallacin Juma’ar garin jim kadan kafin fara Salla sannan ya rantse cewa ba ya taimaka wa ayyukan ta’addanci.

Ko a ranar Litinin din da ta gabata sai dai wasu fusatattun mazauna yankin suka kai hari kan fadar Hakimin bayan sun zarge shi da ba bata-gari mafaka.