Home Labaru Damben Boksin: Oleksandr Usyk Ya Zama Sabon Zakaran Duniya

Damben Boksin: Oleksandr Usyk Ya Zama Sabon Zakaran Duniya

13
0

Oleksandr Usyk ya zama sabon zakaran damben boksin na duniya ajin babban nauyi bayan da ya lallasa mai riƙe da kambu Anthony Joshua dan Birtaniya kuma asalin Najeriya, a karon battar da aka yi jiya a London.

Sabon zakaran dan Ukraine ya yi wasan kura da Joshua ne a gaban ‘yan kallo dubu 65, a filin wasa na kungiyar Tottenham Hotspur, da ke arewacin London a damben na turmi 12.

Dukkanin masu bayar da maki su uku, sun bai wa Usyk nasara a kan Joshua inda sakamakon ya kasance – 117 da 112, sai 116 da 112, sannan kuma da 115 da 113.

Wannan shi ne karo na biyu da aka taba doke Anthony Joshua a matsayin sa na kwararren dan damben boksin.