Wasu kasashen kungiyar Tarayyar Turai 6 sun amince da karbar ‘yan cirani 356 wadanda jirgin ruwan Ocean Viking mallakin kasar Norway ya ceto a tekun mediterranean karkashin jagorancin kungiyoyin agaji na MSF da SOS.
Rahotanni sun bayyana cewa tsakankanin ranakun 9 zuwa 12 ga watan nan ne, kungiyoyin agajin biyu suka yi nasarar ceto ‘yan ciranin daga kananan jirage 4 lokacin da suke kokarin tsallakawa nahiyar Turai ta tsakiyar tekun Mediterranean daga Libya.
Kassahen da suka amince
da karbar ‘yan ciranin sun hada da Faransa, da Jamus, da Ireland, da Luxembourg,
da Portugal, da kuma Romania.
You must log in to post a comment.