Home Labaru Yaki Da Rashin Gaskiya: Gwamnatin APC Ta Ba ‘Yan Nijeriya Kunya –...

Yaki Da Rashin Gaskiya: Gwamnatin APC Ta Ba ‘Yan Nijeriya Kunya – Usman Bugaje

342
0

Tsohon Mai ba shugaban kasa shawara Dakta Usman Bugaje, ya ya ce ya fahimci akwai matsala a tsarin tafiyar gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari na yaki da rashin gaskiya.

Usman Bugaje, ya bayyana yakin da gwamnatin APC ke yi da marasa gaskiya a matsayin abin kunya, inda ya zargi Miyagun ‘Yan siyasa da hannu a rikicin Makiyaya da Manoma.

Bugaje ya kara da cewa, wasu ‘Yan siyasa da ba su iya cin zabe sai ta hanyar hada al’umma fada da sunan addini da kabilanci ne su ke ruruta wutar rikicin Makiyaya da Manoma.

Dakta Bugaje ya bayyana haka ne, yayin da ya ke jawabi a wajen bikin taya Sarkin Fulanin Legas Dakta Mohammed Abubakar Bambado II murnar shafe shekaru 25 a kan gadon sarauta.

Tsohon ‘Dan majalisar wakilan, ya kuma koka da halin da ake ciki na rashin aikin yi, inda ya ce idan ba a gaggauta daukar mataki ba Nijeriya za ta samu kan ta a cikin mawuyacin hali.

Ya ce dole jama’a su damu, ganin yadda aka kasa samun nasarar yaki da barayin gwamnati, ya na mai bayyana yaki da rashin gaskiyar da ake yi a matsayin abin da ya ba su matukar kunya.

Leave a Reply