Home Labaru Tsaro: ‘Yan Sanda Sun Kama Wadanda Su Ka Yi Garkuwa Da Dan...

Tsaro: ‘Yan Sanda Sun Kama Wadanda Su Ka Yi Garkuwa Da Dan Jarida A Abuja

410
0

Rundunar ‘yan Sandan Nijeriya, ta bada sanarwar kama wasu mutane su uku da ta ke zargi da hannu wajen yin garkuwa da dan jaridar da ke aiki a Gidan Talbijin na Channels a Abuja.

Wadanda ake zargin da sun sace Friday Okeregbe, wanda dan rahoto ne a gidan talbijin na Channels, amma su ka sake shi bayan ya shafe kwanaki shida a hannun su.

Wadanda aka kama kuwa sun hada da wani Hanniel Patrick, da Abdulwahab Isah da Salisu Mohammed.

A cikin wata sanarwa da Kakakin Rundunar ‘yan Sandan Nijeriya Frank Mba ya fitar, ta ce an kama wadanda ake zargin ne tun a ranar 9 watan Afrilu.

Ya ce ‘yan ta’addan sun kama Okeregbe, sun kuma boye shi a wata maboyar masu garkuwa da mutane a garin Karmo da ke gefen Abuja.

Mba ya ce an samu bindiga kirar gargajiya, da harsashen bindiga AK 47 uku, da gatari, da wayoyin hannu, da hulunan rufe wa wadanda su ka kama fuska da sauran kayayyaki a hannun su.