Home Labaru Bakunci: Shugaba Buhari Zai Tarbi Zababbun ‘Yan Majalissar Wakilai A Fadar Sa

Bakunci: Shugaba Buhari Zai Tarbi Zababbun ‘Yan Majalissar Wakilai A Fadar Sa

313
0
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai karbi bakunci zababbun ‘yan majalissar wakilai a fadar sa da ke Abuja.

Taron dai, zai gudana ne bayan shafe kwanaki 21 da karbar bakuncin zababbun ‘yan majalisar dattawa na jam’iyyar APC da shugaban kasar ya yi.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, taron zai gudana ne tare da shugaban jam’iyyar APC na kasa Adams Oshiomhole da kuma wasu ‘yan kwamitin gudanarwa na jam’iyyar.

Idan dai ba a manata ba, jam’iyyar APC ta fito karara ta nuna sha’awar ta ga Femi Gbajabiamila da take so ya zama kakakin majalisar, sai dai a wannan taro ana kyautata zaton jam’iyyar za ta bayyana dan takarar ta na kakakin majalisar.

Wata majiya daga fadar shugaban kasa ta ce, alamu sun tabbatar da cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari zai fara sabuwar gwamnatin sa ne da wani salo na sallamar daukacin ministocin sa, amma zai akwai yuwuwa ya bar daya ko biyu a cikin su,