Home Labaru Yaki Da Ta’addanci: Sojojin Najeriya Da Na Kamaru Sun Kashe ‘Yan Boko...

Yaki Da Ta’addanci: Sojojin Najeriya Da Na Kamaru Sun Kashe ‘Yan Boko Haram 27

719
0

Mahukunta hukumar Sojin Nijeriya, sun ce a ci-gaba da hare-haren hana Boko Haram samun damar yin barci, sun bindige ‘yan ta’adda 27 a wani farmakin hadin gwiwa da aka kai tare da sojojin kasar Kamaru.

An dai kai farmakin ne a ranar Asabar da ta gabata, kuma an samu manyan makamai da harsasai da kayan sojoji a hannun su kamar yadda mai magana da yawun rundunar sojin ya bayyana.

Ya ce an gwabza yakin ne a kauyukan Wulgo da Tumbuma da Chikun Gudu da Bukar Maryam da ke kan iyaka tsakanin Nijeriya da Kamaru.

Kakakin ya ce, farmakin da aka kai wani yanki ne daga kokarin kakkabe sauran burbushin ’yan ta’addar da su ka rage gaba daya.

Ya ce an kwato motocin harba manyan bindigogi biyar, da baburan hawa masu yawa, da bindigogi samfurin AK47 guda biyar, da kuma manyan bindigogin harbo jiragen yaki guda biyu, da motoci da sauran makamai.

Kakakin sojoji Sagir Musa, ya ce ba a samu ko da sojin Nijeriya ko na Kamaru daya da ya rasa ran sa ko ya ji rauni ba.

Leave a Reply